Inda yar fim din Hausa ce tayi wannan tsiyar ta yar Ganduje da Kaji ana zagi da tofin Allah tsine – Fati Muhammed
Tsohuwar shahararriyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa, Fati Muhammad ta caccaki auren yar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje wanda akayi a makon da ya gabata.
A cewar Fati da ace yar fim ce ta aikata tsiyar da akayi a bikin yar Ganduje da an zage su tare da yi masu tofin Allah tsine.
Ta bayyana su a matsayin azzalumai kawai, sannan ta ce inda Rahma Sadau ko Ummi Zee Zee ne suka yi haka da tuni a soke su.
Ta kuma yi ba’a inda ta ce ina yan Hizbah suke, kodai dama aikinsu akan marasa gata suke yi.
Daga karshe Fati ta ce Ganduje ya ci amanar Musulunci dominana masa kirari da khadimul islam.
KU KARANTA KUMA: Fayose ya ajiye kudirin takarar shugabancin kasa, yana hararar kujerar Osinbajo
Tsohuwar jarumar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa: “AZZALUMAI KAWAI
"Inda yar fim din Hausa ce tayi wannan tsiyar da Kaji ana zagi da tofin Allah tsine – Fati Muhammed .
"Amma da yake yar gidan Gwamna ce da dabba Gwamna shiru KAKEJI..
"GANDUJE kaci amanar addinin musulunci domin Kaine ake maka kirari da khadimul islam. Duba kaga yadda yarka take...
"Inda RAHMA SADAU ce Ko UMMI ZEE ZEE sukayi Haka da tuni Kaji ana tsine mana.....
'"YAN HIZBAH Kuna ina? Ko dama aikin akan marasa gata kukeyi"
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng