Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya

Jiya mu ka ji daga Iyalan sa cewa Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Aliyu Akwe Doma ya riga mu gidan gaskiya bayan 'Yar jinya da yayi na rashin lafiya a wani asibiti a Kasar Israila.

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya
Aliyu Akwe Doma na Jihar Nasarawa ya cika yana shekaru 75

Don haka ne mu ka kawo maku Takaitaccen tarihin Marigayi kamar yadda aka kawo a shafin Pulse Najeriya

1. An haifi Aliyu Domain ne a Ranar 1 ga Watan Satumba na shekarar 1942 a Garin Doma

2. Aliyu Doma yayi karatu a Jamia'ar Ibadan daga 1964 zuwa 1966. Bayan nan yayi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya.

3. Tsohon Gwamnan ya kuma yin Digiri na Masters a 2002 a wata Jami'ar Ambrose Ali da ke Ekpoma a 2002.

4. Marigayin babban Ma'aikacin Gwamnati ne wanda ya kai har matsayin Sakataren din-din-din a 1983.

5. Akwe Doma ya taba zama Mataimakin Gwamnan tsohuwar Jihar Filato. A 2007 ya zama Gwamnan Nasarawa kafin Gwamna mai-ci Tanko Al-Makura ya kada shi a 2011.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng