Nigerian news All categories All tags
Da duminsa: Jirgin yakin soji dauke da dakaru 32 ya yi hatsari, dukkan su sun mutu

Da duminsa: Jirgin yakin soji dauke da dakaru 32 ya yi hatsari, dukkan su sun mutu

Wani jirgin yakin sojin kasar Rasha dauke da fasinjoji 32 ya yi hatsari tare da kashe dukkan mutanen dake ciki.

Jirgin yakin Rasha dauke da dakarun soji 32 ya yi hatsari a Khmeimim ta kasar Siriya.

Rahotanni sun bayyana cewar jirgin ya yi hatsarin ne yayin da yake kokarin sauka a sansanin sojin kasar Rasha dake kasar ta Siriya.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na ranar yau, Talata, 6 ga watan Maris.

Da duminsa: Jirgin yakin soji dauke da dakaru 32 ya yi hatsari, dukkan su sun mutu

Jirgin yakin soji

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta tabbatar da mutuwar dukkan mutanen dake cikin jirgin.

DUBA WANNAN: Duk adawar mai adawa da hassadar mai hassada sai ya yaba mana a kan tsaro - Buhari

Rahotanni sun bayyana cewar jirgin ya yi hatsari ne sakamakon tangarda da ya samu.

A yau ne dai kasashen Turai su ka bayyana niyyar su ta yin wani taro na musamman domin tattauna batun tsaro a kasar Siriya mai fama da tashe-tashen hankula.

Kasar Siriya ta dade tana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci wadanda su ka rikide zuwa matakin yaki. Kasashen turai sun jibge sojoji masu dumnin yawa domin kawo karshe aiyukan 'yan tawaye a kasar amma har yanzu al'amura a kasar basu lafa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel