Ma’aikatan tsaron jami’ar ABU sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane su biyu

Ma’aikatan tsaron jami’ar ABU sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane su biyu

- Jami’an tsaron jami’ar ABU sun yi bajakolin wasu mutane biyu das u ka ce sun addabi makarantar da kewaye da aiyukan ta’addanci

- Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar wadanda aka damke din; Halliru Sani da Abdullahi Musa, mazauna Samaru da Bomo ne

- Jami’an tsaron sun ce wani Dakta Keku Philiph ne ya fara shigar da korafin cewar wasu matasa na yiwa rayuwar sa barazana

A jiya litinin ne jami’an tsaron jami’ar ABU su ka yi bajakolin wasu mutane biyu da su ka ce sun addabi makarantar da kewaye da aiyukan ta’addanci da ya hadar da satar mutane.

Jami’an tsaron jami’ar sun ce wani Dakta Keku Philiph ne ya fara shigar da korafin cewar wasu matasa na yiwa rayuwar sa barazana kuma nan da nan su ka shiga aiki bayan samun bayanai daga wurin sa.

Ma’aikatan tsaron jami’ar ABU sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane su biyu
jami’ar ABU

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar wadanda aka damke din su biyu; Halliru Sani; mai shekaru 25 dake zaune Samaru da Abdullahi Musa; mai shekaru 30 dake zaune a Bomo, sun amsa laifin da jami’an tsaron ke tuhumar su das hi.

DUBA WANNAN: Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC, ta yi gum a kan yiwa maigidanta kamfen

Da yake magana da manema labarai, shugaban jami’an tsaron jami’ar, Kanal Jibril Tanko (mai ritaya), ya bayyana sun dade suna fakon masu laifin kafin daga bisani su yi nasarar cafke su. Kazalika y ace wadanda aka kama din tuni su ka amsa laifin su, a saboda haka yanzu ba zargin su ake yi ba.

Tanko ya yi godiya godiya ga jamian tsaro na farin kaya da kuma jami’an tsaron makarantar bisa irin rawar das u ka taka wajen kama masu laifin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ngs

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng