An kuma kashe mutane 5 a wani sabon rikici a Jihar Benuwe
- Makiyaya sun hallaka mutane akalla 5 a wani gari a Benuwe
- An yi wa mutanen Garin Umenga kwantan-bauna ne a hanya
- Duk da Jami’an Sojin da aka kawo ba a fasa wannan ta’adi ba
Kwanan nan an kuma kashe mutane 5 a wani sabon harin da aka kai a Jihar Benuwe bayan da wasu Makiyaya su ka dura Garin Umenga. Jami’an Gwamnatin na Jihar Benuwe sun tabbatar da wannan hari yanzu haka.

Labari ya zo mana daga Vanguard cewa an hallaka akalla mutum 5 bayan da wasu da ake zargi Makiyaya ne su ka kai hari a Karamar Hukumar Guma duk da Jami’an tsaron da aka baza domin kawo tsanaki a Yankin.
KU KARANTA: Shehu Sani ya kuma caccakar Gwamnatin Shugaba Buhari kan tsaro
Ba wannan ne karo na farko da aka kai hari wannan Gari ba don kuwa a farkon shekarar nan an yi kokarin hallaka mutanen da ke wannan Gari sai dai an tsaga da ragowar kwana. Wannan karo dai Makiyayan sun yi barna.
Mutum 1 ne kurum ya tsere ya kuma yi rai cikin wadanda aka kai wa harin kamar yadda mu ka ji. Ana zargin Makiyayan sun yi kwantan-bauna ne inda su ka budawa mutanen Garin wuta yayin da su ke hanyar komawa gidajen su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng