Za a takawa tsofaffin Gwamnonin da ke karbar fansho burki a Najeriya
- An nemi a daina biyan tsofaffin Gwamnonin Najeriya da Mataimakan su fansho
- Kungiyar ACF tace sam bai dace ana biyan tsofaffin Gwamnoni wannan kudi ba
- Wasu tsofaffin Gwamnonin da ke Majalisa na cin albashi biyu kenan a Najeriya
Mun samu labari cewa ana yunkurin takawa tsofaffin Gwamnonin Najeriya da ke dibar fansho burki. Kwanan nan Jihar Kwara ta kawo irin wannan kudiri a Majalisar dokokin Jihar. Kungiyar ACF ce ta fitar da wannan matsaya kwanan nan.
Kungiyar Dattawan Arewa watau ACF tayi kira ga Majalisun dokoki na Jihohi da su yi kokarin dakatar da biyan tsofaffin Gwamnoni da Mataimakan su makudan kudi da sunan fansho. Sakataren yada labarai na ACF ya bayyana wannan.
KU KARANYA: Gwamna El-Rufai yace Sanata Shehu Sani jahili ne
Muhammad Biu ya fitar da jawabi inda kungiyar ACF ta yabawa Majalisar Jihar Kwara na daina biyan tsofaffin Gwamnoni da Mataimakan su wasu kudi na fansho. Wasu tsofaffin Gwamnonin ma dai kar hada albashi sama da guda a kasar.
Kungiyar ta Arewa tace bai dace a rika ba Gwamnonin da su ka bar kujera makudan kudi ba yayin da wadanda su kayi wa kasa aiki su kayi ritaya kan sha da kyar. Bayan nan ma dai kuma kasar na fama cikin wani hali na tattalin arziki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng