Sheikh Ahmad Gumi yayi tir da barnar dukiyar da aka yi wajen daurin auren ‘Ya ‘yan Gwamna
Malamin addini Sheikh Gumi ya soki almubazzarancin Shugabannin kasar nan. Shehin yace duk da N50, 000 ne kurum sadakin auren diyar Ganduje, an yi wahala an kuma barnatar da makudan Dukiyoyi wanda ya nemi Shugabanni su tsaya su yi wa Talakawa aiki.
Mun samu labari cewa Babban Malamin Addinin Musulunci na kasar nan Sheikh Ahmad Abubakar Gumi yayi kaca-kaca da Shugabanni da sauran masu mulki na Najeriya na barnar dukiya wajen bikin auren ‘Ya ‘Yan Gwamna.
Idan ba ku manta ba a makon nan ne ‘Diyar Gwamnan Kano Fatima Ganduje ta auri ‘Dan Gwamnan Jihar Oyo Idris Abiola Ajimobi inda manyan kasar nan daga ko ina su ka cika Garin Kano domin halartar wannan daurin auren.
KU KARANTA: Dattawan Kano sun yi tir da wasu Kalaman Kwankwaso
Sheikh Ahmad Abubakar Gumi yace addinin Musulunci bai yarda da barna da dukiyar al’umma ba inda yace abin da ake bukata wajen daurin aure kurum shi ne tsirarrun shaidu amma ba Shugabanni su kona man jirgi ba don zuwa biki.
Malamin na kasar ya kuma yi tir da yadda Amaren su ka rika daukar hotunan da ba su dace ba ana yadawa. A cewar Shehin, idan Shugabanni su ka lalace to Ubangiji na shirin hallaka al’umma ne don haka yace dole su yi wa’azi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng