'Yan Arewa sun koka da Gwamnatin APC; sun ce Shugabanni sun yaudare su

'Yan Arewa sun koka da Gwamnatin APC; sun ce Shugabanni sun yaudare su

- Kungiyar Arewa yayi tir da Gwammnatin APC mai ci a yanzu

- Kungiyar da ke Yankin Shugaban Kasar tace an ci amanar su

- Haka zalika an zargi Gwamnatin Jihar da rashin tsare rayuka

Mun samu labari daga Jaridar Sahara Reporters cewa wata Kungiya ta 'Yan Arewa mai suna CNG ta bakin mai magana da yawun bakin Kungiyar ta soki Gwamnatin Buhari inda tace ya ci amanar jama'a ganin irin abin da ya faru kwanan nan.

'Yan Arewa sun koka da Gwamnatin APC; sun ce Shugabanni sun yaudare su
An yi kaca-kaca da Shugaban kasa Buhari na zuwa biki a Kano

Abdulaziz Sulaiman wanda shi ne mai magana da bakin Kungiyar nan ta hadakar 'Yan Arewa tayi tir da yadda Shugaban kasar da sauran manyan Najeriya su ka rusa Kano zuwa wajen daurin diyar Gwamnan Jihar duk da halin da ake ciki a wasu wurare.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya Buhari na halartar biki a Kasar Ghana

CNG ta bayyana cewa Shugaba Buhari ya nuna rashin tausayi na kyale mutanen da aka kashe a Mambila amma ya wuce wajen biki tare da sauran manyan kasar. Kungiyar tace Gwamnonin da ya dace shi tsare jama'a su ma sun bar aikin gaban su.

Kungiyar dai ta tunawa Gwamnatin APC irin abin da ya faru lokacin da Boko Haram su ka kashe Jama'a amma Shugaba Jonathan ya buge da yawon siyasa. Yanzu dai dole ta sa Shugaban kasar ya kai ziyara Jihar Taraba kuma zai leka sauran wurare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel