Abu daya da har yanzu nake nadama a rayuwa - Obasanjo

Abu daya da har yanzu nake nadama a rayuwa - Obasanjo

- Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji da kuma farar hula, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce har yanzu akwai abinda yake nadama

- Obasanjo, mai shekaru 81 a duniya, ya ce ya so a ce iyayen sa sun yi nisan kwana domin ganin irin nasarar da ya samu a rayuwa

- Obasanjo ya ce yana matukar bankincikin mutuwar wuri da iyayen sa su ka yi

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji da farar hula, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewar har yanzu akwai wani abu dake matukar damun sa duk lokacin da ya tuna da shi.

Obasanjo, mai shekaru 81 a duniya, ya ce babban abinda yake nadama da takaici shine rashin dogon kwanan iyayen sa.

Obasanjo na wadannan kalamai ne a yau, Litinin, yayin da ya cika shekaru 81 da haihuwa.

Abu daya da har yanzu nake nadama a rayuwa - Obasanjo
Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya ce, ya so a ce iyayen sa sun yi nisan kwana domin ganin irin nasarorin da ya samu a rayuwa.

"Wani abu daya da nake matukar nadama da takaicinsa shine yadda iyayena su ka mutu da wuri. Basu tsaya sun ci moriyar wahalar da su ka sha a kaina ba. Na so a ce sun yi nisan kwana, sun ci moriyar wahalar su," inji Obasanjo.

Obasanjo ya ce ya yarda da karin maganar nan Yoruba da su ke cewa "wadanda su ka mutu na yin waiwaye domin ganin abinda su ka bari a duniya".

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta bayar da tallafin miliyan $10, kayan agaji ga Najeriya

Obasanjo ya kara da cewar, riko da wannan karin magana ne kawai ke kwantar ma sa da hankali, domin a cewar sa, ya san iyayen sa na cikin farinciki a kabarinsu, yayin da suke kallon irin nasarorin da ya samu a rayuwa.

Obasanjo ya ce zai cigaba da bautawa Allah da yin addu'o'i ga iyayen sa. Kazalika yayi godiya ga hadiman da da kuma mataimakan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel