Da dumi-dumi: Dalibai 2 sun mutu, 98 sun jikkata a hadarin motan makaranta

Da dumi-dumi: Dalibai 2 sun mutu, 98 sun jikkata a hadarin motan makaranta

Daliban makarantan Our Lady of Fatima School, Kuru, da ke garin Jos sun rasa rayukansu a wani mumunan hadari da motan makaranta yau Litinin, 5 ga watan Maris, 2018.

Wani jami’in hukumar FRSC da ya shaida wannan ibtila’I ya bayyanawa manema labarai cewa wannan abu ya faru da safen nan ne a titin Mararaba-Jama’a sanadiyar lalacewan birki.

“Wani jami’in makarantan ya bayyana cewa: “Dalibai 100 ke cikin motan da malamai 7; biyu daga cikin daliban sun mutu, wadanda suk aji rauni an kaisu asibiti”

An kai 18 daga cikin yaran asibitin Our Lady of Fatima Hospital, Jos, 76 zuwan asibitin Plateau Specialist Hospital, Jos, 4 kuma an kaisu asibitin Bukuru Specialist Hospital.

Da dumi-dumi: Dalibai 2 sun mutu, 98 sun jikkata a hadarin motan makaranta
Wannan ainihin hoton bane

Gwamnan jihar, Sinon Lalong, ya kai ziyara ga wasu daga cikin yaran da aka kai asibitin jihar Flato.

KU KARANTA: Buhari na halartan bikin samun ‘yancin kasar Ghana a yau Litinin

Kwamishanan labaran jihar, Mr Yakub Dati, ya bayyana cewa gwamnan ya yi alkawarin biyan kudin asibitin dukkan wadanda wannan abu ya shafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng