Gwamnatin Tarayya na shirin gina gidajen Naira Biliyan 1.3 a Sokoto

Gwamnatin Tarayya na shirin gina gidajen Naira Biliyan 1.3 a Sokoto

- Gwamnatin Buhari na shirin kammala gina wasu gidaje a Jihar Sokoto

- Bayan nan kuma Gwamnatin Tarayya za ta gina gidaje 500 duk a Jihar

- Akwai kuma hanyoyin da Ministan ayyuka ya nemi ayi maza a kammala

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta gina gidaje na sama da Naira Biliyan 1.3 a Jihar Sokoto. Ana sa rai nan da ‘yan makonni Gwamnatin Tarayyar kasar ta kammala aikin a kuma shiga wani inda za a gina gidaje 500.

Gwamnatin Tarayya na shirin gina gidajen Naira Biliyan 1.3 a Sokoto
Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanonin Najeriya kwangilar ginin gidaje

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnatin Tarayya ta hannun Ministan gidaje, lantarki da ayyuka na shirin gina gidaje 80 a Garun Kwannawa da ke Karamar Hukumar Dange Shuni a cikin Jihar Sokoto. Wannan aiki zai ciki kudi har sama da Naira Biliyan 1.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari yayi magana kan 'Yan matan da aka sace

Babatunde Fashola wanda shi ne Ministan gidaje, lantarki da ma ayyuka na kasar ya bayyana wannan lokacin da wani babban Darektan ya wakilce sa a wata ziyara Sokoto inda yace yanzu an fara neman ‘yan kwamgila na cikin gida har kamfanoni 20 da za a ba wannan aiki.

Ministan ya bayyana cewa za a ba kamfanonin cikin gida wannan aiki domin zaburar da su. Hakan kuma zai ba matasan Najeriya da dama hanyar samun abinci. Bayan nan akwai hanyoyin da Ministan ya bada umarni a kammala irin titin Sokoto zuwa Jega da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel