Masu bincike sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau
- Masana kimiyya sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau a kasar Amurka
- Masu bincke sun ce sun yi amfani da birai wajen fitar da sabuwar maganin cutar kanjamau
Masu bincike a bangaren kiwon lafiya sun gano maganin da zai rage karfin kwayar cutar kanjamau na tsawon watanni shida
Binciken da masana kimiyya suka gudanar a taron samar da magungunan zamani karo na 25 a birnin Boston dake kasar Amurka sun ce sun yi amfani da birai wajen fitar da maganin.
Masu bincike sunce birai shida daga cikin birai 12 da sukayi amfani da su wajen gudanar da bincken sun warke bayan sun yi musu amfani da kyawar maganin da suka binciko.
KU KARANATA : Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari
Sun ce nan ba da jimawa ba, za su fara yiwa 'yan Adam gwajin maganinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng