Da arziki a garin wasu, gwara a garinku: Manyan Kamfanonin sarrafa shinkafa na kasar Thailand zasu dawo Najeriya

Da arziki a garin wasu, gwara a garinku: Manyan Kamfanonin sarrafa shinkafa na kasar Thailand zasu dawo Najeriya

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa wasu daga cikin hamshakan kamfanonin sarrafa shimkafa a kasar Thailand sun kammala shirin dawo da kamfanoninsu zuwa Najeriya don sarrafa shinkafar a nan gida Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito ministan watsa labaru, Alhaji Lai Muhammed ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris a yayin ziyarar da ya kai jihar Kebbi don ganin cigaba da ake samu a sha’anin noman shinkafa.

KU KARANTA: Hotunan shahararren dan siyasan Kano da ya tsira da harbin bindiga daga wajen masu garkuwa da mutane

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan na fadin hakan na nufin gwamnatin Najeriya ta samu nasara akan kamfanonin kasashen waje kenan, musamman ma na kasar Thailand, daga inda mafi yawancin shinkafar da ake ci a Najeriya ke fitowa.

Da arziki a garin wasu, gwara a garinku: Manyan Kamfanonin sarrafa shinkafa na kasar Thailand zasu dawo Najeriya
Manoman shinkafa

“A yanzu haka, kamfanonin sarrafa shinkafa na kasar Thailand na neman hadin kan gwamnatin Najeriya don samun izinin karkato da ayyukansu na sarrafa shinkafa zuwa Najeriya, inda zasu kafa kamfanonin sarrafa shinkafar.”

Da yake karin haske kan musabbabin da ya sa kamfanonin zasu shigo Najeriya, Minista Lai yace hakan na da nasaba ne da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigo da shinkafa, wanda hakan ya rage shigo da shinkafa daga kasar Thailand da kasha 90.

Ministan yace Najeriya ta rage shigo da shinkafa daga kasashen waje, daga tan 20,000 zuwa tan 644.000 tun bayan fara aiki na dokar hana shigo da shinkafa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng