Ku zabi mutanen kirki ba wadanda ke raba kudi ba – Inji Jikar Tafawa-Balewa

Ku zabi mutanen kirki ba wadanda ke raba kudi ba – Inji Jikar Tafawa-Balewa

- Jikar Marigayi Tafawa-Balewa tayi kira ga jama’a kan shugabanci

- Hajiya Hajara Yakubu tace a guji zaben mutanen da ba na kirki ba

- Baiwar Allah tace wasu su na siyasa ne don samun dukiya kurum

Mun samu labari cewa wata Jikar tsohon Shugaban Najeriya na farko Sir Abubakar Tafawa-Balewa ta ba ‘Yan Najeriya shawara game da wanda za su zaba su shugabance su nan gaba.

Hajara Yakubu-Wanka wanda jika ce wajen Marigayi Shugaba Tafawa-Balewa ta shawarci Jama’a a Garin Yankanaji da ke cikin Karamar Hukumar Toro a cikin Jihar Bauchi da su zabi mutane masu mutunci da kima wanda za su kawo gyara a kasar.

KU KARANTA: APC ta nemi Shugaban kasa Buhari ya tsaya yayi aiki

Hajiya Hajara tace sai lokaci da aka zabi nagari sannan rayuwar Talaka za ta inganta na din-din-din. Jikar tsohon Shugaban na Najeriya ta nemi Jama’a su guji zaben wadanda ke ba su abin hannu na ‘dan lokaci domin ba za a taba ganin cigaba ba.

Yakubu Wanka ta gargadi Jama’a da cewa masu bada abin hannu kafin zabe mayaudara ne kurum kuma sun dauki siyasa a matsayin kasuwancin da za su ci riba maimakon yi wa kasa hidima. Hajiya Hajara dai tana da gidauniya da take taimakawa marasa galihu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng