An yaye wasu sababbin Sojojin sama 5 da su kayi karatu a cikin gida

An yaye wasu sababbin Sojojin sama 5 da su kayi karatu a cikin gida

- Sojojin saman Najeriya ta yaye wasu yaran ta a Garin Maiduguri

- Wannan ne karo na farko da aka horas da matuka jirgi a Najeriya

- Shugaban Hafsun Sojin sama ne ya karawa Sojojin lambar girma

Rundunar Sojojin saman Najeriya ta bakin Olatokumbo Adesanya tace ta yaye wasu sababbin Sojoji da su kayi katatun su su ka gama ba tare da fita kasar waje ba. An yi bikin yaye sababbin Sojojin ne a Garin Maiduguri.

An yaye wasu sababbin Sojojin sama 5 da su kayi karatu a cikin gida
Sababbin matuka jirgin yakin da aka horas a Najeriya

Wadannan Sojoji 5 sun yi karatun ne a Makarantar Sojojin sama da ke Kaduna inda su ka karanci harkar tukin jirgi na kusan shekaru 2. Sojojin sun kuma kware a sauran kwas da su ka hada da sanin kayan aiki n jirgin yaki da sauran su.

KU KARANTA: An kashe mutane 20 da dabbobi rututu a Jihar Taraba

Gwamnatin nan na kokarin ganin ba a bar Najeriya ita ma a baya ba. Wannan ne dai karo na farko da aka horas da matuka jirgi a cikin Najeriya har su ka kamalla kwas din su. Wadannan Sojoji za su yi amfani a Yankin Boko Haram.

Sababbin Sojojin sun yi amfani da wasu jiragen yaki da ake ji da su na CH-3A RPA. Ana aiki da wannan jirgi wajen kai wa ‘Yan ta’addan Boko Haram hari a Yankin Arewa-maso-gabas. Yanzu haka dai za a kara horas da wasu Sojojin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng