Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya tonawa kan sa asirin abin da ya faru a 1975

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya tonawa kan sa asirin abin da ya faru a 1975

- Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wata tsiya da ya taba tsulawa a baya

- Tsohon Shugaban kasar ya taba korar Amurkawa daga ofishin su a Legas

- Obasanjo ya karbe gidan ne ya ba Abokin sa Ahmadu Ali domin ya zauna

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya fallasa kan sa da kan sa inda bayyana wata barna da yayi sama da shekaru 40 da su ka wuce. Wannan dai ya sa har manyan sa su kayi ta yi masa fada a wancan lokaci.

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya tonawa kan sa asirin abin da ya faru a 1975
Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wata tsiya da yayi

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a shekarar 1975, Ministan Ilmi na kasar a lokacin Kanal Ahmadu Ali ya taba zuwa wajen sa neman taimako. Ali yana nema ne a ba shi wani katafaren gida ne a kusa da filin tsere a cikin Legas domin ya rika zama.

KU KARANTA: PDP ta jinjinawa tsohon Shugaban kasa Obasanjo

Sai dai kuma a lokacin wasu Fararen fata ne ‘Yan kasar Amurka a cikin wannan gida inda su ke wani aiki. Duk da wannan bai hana Obasanjo fatattakar bakin kasar ba. Obasanjo ya hada kai da Ahmadu Ali aka sa Sojoji da asuba aka tsare gaban ginin.

A lokacin da wadannan mutane su ka zo aiki da safe, sai su ka iske Sojoji jige kuma aka hana su shiga. Wannan ya sa aka yi ta rikici kuma har alaka ta tabarbare tsakanin Gwamnatin Sojan Gowon da kuma Kasar Amurka da ma samun sabani tsakanin sa da Gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng