Ganduje ya bawa Ajimobi mamaki bayan ya nemi a biya N50,000 a matsayin sadakin auren diyar sa
- A jiya ne aka daura aure tsakanin dan gwamnan jihar Osun, Ajimobi, da diyar gwamna, Ganduje, a jihar Kano
- Yayin daurin auren, gwamna Ganduje, ya nemi iyayen ango su biya N50,000 a matsayin sadakin auren diyar sa, Fatima
- Gwamna Ajimobi, uban ango, ya kasa boye mamakin sa a kan arahar kudin sadaki a arewacin Najeriya
Auren da aka daura a jiya tsakanin dan gwamnan jihar Oyo, Isiaka Ajimobi, da diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bawa 'yan kabilar Yoruba mamaki.
Gwamna Ganduje cikin murna da farincikin ganin yadda manyan mutane daga fadin kasar nan su ka yi tururuwa domin shaida daurin auren, ya yanke N50,000 a matsayin kudin sadakin auren diyar sa, Fatima.
"Dan ka zai biya N50,000 a matsayin sadaki," Ganduje ya shaidawa Ajimobi.
Cikin mamaki gwamna Ajimobi ya sallame ya sanar da ubangiji, "Laa'ilaha Ilalahu!, haka aure yake da araha a arewa? Don Allah ku karawa da na, Idris, kudin sadaki."
DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari
Wannan kalami na Ajimobi ya jawo barkewar dariya a tsakanin manyan mutanen dake wurin daurin auren.
Saidai madaurin auren 'ya'yan gwamnonin, mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya share wannan bukata ta Ajimobi tare da daura aure tsakanin Idris Ajimobi da Fatima Ganduje.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya zama waliyyin ango, yayin da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya zama waliyyin amarya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng