Nigerian news All categories All tags
Gidajen mai 2,200 dake iyakokin Najeriya ke tsotse man fetur da kawo wahalar man

Gidajen mai 2,200 dake iyakokin Najeriya ke tsotse man fetur da kawo wahalar man

- ABUN MAMAKI AN GANO AKWAI GIDAJEN MAI 2,201 A GARURUWAN BAKIN BODAR NIJERIYA

- Akwai gidajen mai 2,201 a garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya da na yankunan bakin Teku, wanda su ke amfanin da man Fetur da ya kai yawan lita miliyan 144.9

Gidajen mai 2,200 dake iyakokin Najeriya ke tsotse man fetur da kawo wahalar man

Gidajen mai 2,200 dake iyakokin Najeriya ke tsotse man fetur da kawo wahalar man

Hakan ya sanya Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya ya busa kararrawa ta yanda ake fita da man zuwa kasashen dake makwabtaka da Najeriya, hakan ya na sanyawa rasa gane abun da ke sawa main ya yi wahala a kasa kuma a ka sa rarraba shi a cikin kasar.

Wanda kamfanin na NNPC ya na kasha sama da $5.8bn don shigo da man tun a watan Disamba, shekara ta 2017. Manyan masu jagorancin kamfanonin sun kai ziyara ga shugaban Kwastan na Najeriya , col. Hamid Ali (Rtd), a ranar 2 ga watan Maris.

Manajan Direkta na NNPC, Dr. Maikanti Baru, ya bayyana cewa binciken da aka kamfanin ya gudanar ya nuna alamar hadin kai tsakanin masu tashar Jiragen Ruwa na Man Fetur da kuma masu Fitar da shi ta barauniyar Hanya.

Dr. Baru ya bayyana cewa, sabili da banbancin kudaden man fetur da ke tsakanin Najeriya da kasashen da makwabtaka da ita, ya zama wajibi a sa ido kan masu safarar man ta barauniyar hanya don hana fita da man a garuruwa da ke iyakar, ya ce hakan ya haifar da matsala ga kasuwar man fetur na Najeriya a dukkan kasashen dake makwabtaka, kamar su Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin, Cameroon, Chadi, da Togo har ma da Ghana wadda ba ta da iyaka da Najeriya.

DUBA WANNAN: Hadimi yayi bayanin yadda ya boye biliyan biyar a uwar dakin Jonathan

Shugaban na Kwastan ya yi godiya ga Shugaban kamfanin na NNPC bisa ga bayanai da yayi da shawarwari kan matakan samar da man fetur, ya kuma ce wannan zai taimaka wurin tsarin aiki don maganace matsalar.

Ya kuma yi kira ga matakan tsaro da su magance matsalar farashin mai wanda shine mahimmin abun da ke kawo fita da man ta barauniyar hanya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel