Nigerian news All categories All tags
Gwamna dan-Kwambo ya halarci auren Kyari, yayi kira da a rungumi zama lafiya

Gwamna dan-Kwambo ya halarci auren Kyari, yayi kira da a rungumi zama lafiya

- Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, a jiya Asabar ya halarci daurin auren diyar Muhammed Kyari, Amina Muhammed Kyari a garin Maiduguri, a jihar Borno

- Muhammed Kyari Darakta ne a ma’aikatar kudi, ta jihar Gombe. Diyar tashi ta auri saurayin ta wanda suka dade tare suna soyayya mai suna Muhammed Baba Shehu, wanda manyan mutane dayawa ska halarta

- Daurin auren ya tara mutanen dayawa, aminnan arziki wanda suka zo daga wurare daban-daban na garin da ma wasu daga Arewacin Nijeriya in da angon ya fito

Gwamna dan-Kwambo ya halarci auren Kyari, yayi kira da a rungumi zama lafiya

Gwamna dan-Kwambo ya halarci auren Kyari, yayi kira da a rungumi zama lafiya

A lokacin da ake ta bukukuwan auratayya da murkususun siyasa a Arewa, gwamna Dankwambo na Gombe, shima ya halarci auren wani dan siyasar a kasar Borno. Sai dai shi dankwambo dann PDP ne, kuma auren bai tara manyan 'yan siyasa ba.

Gwamna Dankwambo wanda shine waliyin Amarya, ya halarci taron tare da ‘yan rakiyar sa, wadan da chairman na Kwami LG, Galadiman Difa, Dukku Local Government Area PDP Chairman, Hon. Ya’u Hassan Marafa, Alh. Baba Bawa, Alh. Ahmadu DK da kuma Dahiru Hassan Kera.

DUBA WANNAN: Hadimi yayi bayanin yadda ya boye biliyan biyar a uwar dakin Jonathan

Gwamnan ya shawarci Ango da Amarya da cewa a koda yaushesu kasance masu son juna, su kuma gina auren su bias amana da girmama juna, bayan haka ya masu fatan alkairi da dukkan ‘yan uwa da abokan arziki. Ya kuma roki Allah da ya sa albarka a cikin auren.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel