Jihar Adamawa: Manyan 'yan siyasa zasu yiwa gwamna Bindo rajamu a 2019
- Gwamnan jihar Adamawa, Muhammadu Umar Jibrilla, na fuskantar adawa mai zafin gaske daga cikin jam'iyyar sa ta APC
- Manyan jagororin jam'iyyar APC na da shakku a kan biyayyar gwamna Bindo ga Buhari duk da ya bayyana hakan karara a fili
- Gwamna Bindo, na hannun damar Atiku, ya ce ba ya tare da tsohon ubangidan nasa a canjin shekar da ya yi zuwa tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP
Wasu manyan 'yan siyasa a jam'iyyar APC a jihar Adamawa na kulle-kullen yadda zasu hambarar da gwamnan jihar, Muhammadu Umar Jibrilla Bindo, daga sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
Duk da gwamna Bindo ya nuna goyon bayan sa ga shugaba Buhari da jam'iyyar APC, jiga-jigai a cikin jam'iyyar a jihar na ganin gwamnan na yin ladabi ne kawai don gyara miya, a saboda haka basu yarda da shi ba.
Jagororin jam'iyyar APC a jihar na zargin gwamnan ne bisa dogaro da kusanci da Atiku da yake da shi. Sai dai gwamna Bindo ya fito fili karara ya bayyana cewar ba ya tare da Atiku a canjin shekar da ya yi zuwa tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP.
DUBA WANNAN: Nakasassu za su ci moriyar tsarin gwamnatin tarayya na samar da muhalli
Daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar APC dake kokarin hada karfi da karfe domin dakatar da gwamnan akwai; tsohon gwamnan jihar, Murtala Nyako, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan, tsohon gwamnan jihar Legas a mulkin soji, Buba Marwa, da sanata Abdulaziz Nyako.
Masu bibiyar siyasar jihar sun ce manyan jagororin jam'iyyar na son maye gurbin gwamna Bindo da daya daga cikin; Nuhu Ribadu, Abdulaziz Nyako, Injiniya Marcus Gubduri, ko kuma Bello dukkan su anyi ittifakin kan iya bawa gwamnan matsala a zaben jam'iyyar na fitar da gwani.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng