‘Yan Boko Haram sun sace ‘yar shekara 24 da ke aikin asibiti a Garin Rann

‘Yan Boko Haram sun sace ‘yar shekara 24 da ke aikin asibiti a Garin Rann

- An samu karin bayani a kan Budurwar da Boko Haram su ka sace

- A makon jiya ‘Yan ta’addan su ka kai hari a cikin garin Kala Balge

- Wannan yarinya tana karatu a Jami’ar Tarayya ta Garin Maiduguri

Mun samu labari na musamman daga Yerwa Express game da yadda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka sace wata Baiwar Allah da ke aiki da Malaman asibiti a Garin Rann a karshen makon can.

‘Yan Boko Haram sun sace ‘yar shekara 24 da ke aikin asibiti a Garin Rann
An sace wannan Baiwar Allah a Garin Rann a Jihar Borno

A Ranar Alhamis ne ‘Yan Boko Haram su ka kai hari a Garin Rann cikin Karamar Hukumar Kala-Balge da ke Jihar Borno inda su ka kashe akalla mutum 8 su ka kuma sace mutum 1 wanda aka gano cewa wata Budurwa ce da ke aikin asibiti.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun kama wasu Makiyaya 3 a Jihar Nasarawa

Wannan yarinya mai suna Hauwa Muhammad Liman tana aiki ne da wata Kungiyar bada agaji ta kasar waje na ‘dan lokaci. Wannan Budurwa dai ba ta fadawa mutanen gidan su inda ta ke aiki ba don kuwa jama’a sun dauka tana Garin Gomburu.

A lokacin da ‘Yan ta’addan su ka iso su na ta faman harbi, wannan Malamar asibiti ta aika sakon sauti zuwa wani ‘Dan uwan ta inda ta rika kukan cewa ga shi nan ana shirin tserewa da su. Shekarar wannan Yarinya 24 kuma ‘Daliba ce a Jami’ar Maiduguri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng