Nigerian news All categories All tags
Auren diyar gwamna: Ba'a ga Hisba ko daya ba, bayan kuwa an baje kuturi a bikin

Auren diyar gwamna: Ba'a ga Hisba ko daya ba, bayan kuwa an baje kuturi a bikin

- An sha biki, bidiri da birede a Kano a jiya

- Hisba sun haramtawa Kanawa badala tsakanin mata da maza

- An gwangwaje an sheqe aya a jihar Hadimul Islama

Auren diyar gwamna: Ba'a ga Hisba ko daya ba, bayan kuwa an baje kuturi a bikin

Auren diyar gwamna: Ba'a ga Hisba ko daya ba, bayan kuwa an baje kuturi a bikin

Manyan jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya ne suka hallara a Kano a jiya, domin bikin diyar gwamna Ganduje Khadimul Islama, da dan gwamna Ajimobi na Oyo, biki na qasaita da aka kashe miliyoyin Nairori.

Bisa al'ada dai, zaka ji Hisba na kame ko tsawatarwa a titunan jihar Kano, domin tabbatar da mulkin shar'ar Islama, tsari wanda jihar ke kai tun 2000. Sai dai wannan karon tsit kake ji, babu su babu alamar su.

DUBA WANNAN: Dalilan da suka sa nake so a rataye masu yada tsana

Su dai abokan Amarya da na ango, da qawayensu, sun mamaye manyan Otal Otal na garin, da wuraren shaqatawa, sun sha kida da rawa, raha da bidiri, inda bidiyo ke nuna yadda aka baje kolin rausaya da walawa.

Hakan ya ja hankalin Kanawa inda suka bazama shafukan sada zumunta don neman bahasin ko ina Sheikh Aminu Daurawa ya shige, ko ma ina aka baro Hadimul Islama da ake wannan badala haka. Duk da dai anyi wa auren fatan albarka.

Ya zuwa yanzu dai, babu wasu bayanai daga gwamnati ko hukumar hisba. Talaka dai shi yaga shariar Islama, mai kudi yana can sama a jirgi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel