'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar dan majalisar jihar Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar dan majalisar jihar Katsina

- Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da matar dan majalisar jihar Katsina, Alhaji Abubakar Suleiman

- An sace amaryar dan majalisar, Mabruka, a gidan dan majalisar dake karamar hukumar Ingawa a jihar

- Dan majalisar ne ya fadi hakan ga gwamna Masari da Minista Sirika lokacin da su ka kai masa ziyarar jaje

Wasu 'yan bindiga da ya zuwa yanzu ba a san ko su waye ba sun yi awon gaba da matar dan majalisar jihar Katsina, Alhaji Abubakar Suleiman, tare da bukatar a basu Naira miliyan N100m kafin su sake ta.

'Yan bindigar sun sace amaryar dan majalisar, Mabruka, a gidan su dake karamar hukumar Ingawa a jihar Katsina.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar dan majalisar jihar Katsina
'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar dan majalisar jihar Katsina

Dan majalisar ya sanar da hakan ga gwamnan jihar Aminu Bello Masari da Ministan kula da hukumar filayen tashi da saukar jiragen sama na kasa, Hadi Sirika, lokacin da su ka kai masa ziyarar jaje.

Da yake bayani ga gwamnan, Tunas, ya bayyana yadda wasu 'yan bindiga masu yawa su ka dira gidan sa tare da yin awon gaba da amarya sa, Mabruka.

DUBA WANNAN: Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

Ya kara da cewar 'yan bindigar sun yi awon gaba da kayayyaki da su ka hada da sarkoki da wayoyin hannu da kuma kudi, sannan kuma sun kira domin neman kudin fansa.

Gwamna Masari ya yi addu'ar Allah ya bayyana ta, ya kiyaye faruwar hakan a gaba.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, DSP Gambo Isah, ya ce zai nemi bayani a kan afkuwar al'amarin bayan an tuntube shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng