2019: Sultan ya umurci musulmi su mallaki katin zabe don shine 'yancin su
- Sarkin musulmi, Sa'ad Abubakar II ya shawarci al'umman musulmi su mallaki katin zabe don da shine za su iya zaben wanda suke so
- Sultan ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya ke jawabi a wajen rufe taron gasar karatun Al-Qurani mai girma kashi na 32 da aka yi a jihar Katsina
- Sultan din kuma ya janyo hankalin shuwagabani su kasance masu tsoron Allah da yiwa kasa addu'a musamman yanzu da muka samu kanmu cikin matsaloli
Sarkin Musulmi kuma shugabanin majalisar koli na harkokin addinin musulunci, Alhaji Sa'ad Abubakar ya shawarci al'umman musulmi da suyi amfani da damar da suke dashi yanzu don yin rajista da karban katin zabe kafin lokacin zaben na 2019.
A jawabin da yayi wajen rufe taron gasar karatun Al-Qur'ani mai girma karo na 32 da aka gudanar a jihar Katsina, Sa'ad yace ta hanyar mallakar katin zaben ne kawai al'umman za su iya zaben wanda suke so ya jagorance su.
DUBA WANNAN: Atiku zai bayyana matsayar takarar sa a sati biyu masu zuwa
A cewarsa, al'ummar musulmi suna da yawa a Najeriya amma sai masu katin zaben ne kawai za su iya kada kuri'a. Hakan ya sa ya shawarci al'umman musulmi su mallaki katin zaben saboda lokacin da za'a a zo neman kuri'ar su sai su bayyana abin da suke so ayi musu.
Ya kuma yi kira ga shuwagabani da al'umma su kasance masu tsoron Allah da yiwa kasa addu'a musamman yanzu da muka tsinci kan mu cikin halin tsaka mai wuya. Ya kuma shawarci shugabani su kara dagewa wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin al'umma.
A jawabin da ya yi wajen taron, gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce lokaci ya yi da shugabani za su sake yiwa almajiranci kallo da idon basira yadda wasu ke amfani da almajiran wajen kuntata wa al'umma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng