Wani Mutum ya mutu saman Itacen Kwakwa a jihar Imo
Tashin hankali ya afku a yankin Umuocha na karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, yayin da aka tsinto gawar wani mai sana'ar Burkutu, Njoku, saman itacen kwakwa a ranar Alhamis din da ta gabata.
Iheanyi Enwerem, wani makwabcin wannan mutum ya shaidawa manema labarai na Southern City News cewa, marigayi Njoku dai ya fita harkar sa ta nema tun da duku-duku domin tatsar ruwan kwakwa na sana'ar sa ta sayar da Burkutu.
Enwerem yake cewa, babu wata alama da tuna cewar marigayi Njoku ba zai dawo gida ba tare da ran sa ba, sakamakon irin karsashi na lafiyar sa.
KARANTA KUMA: Wani Dattijo ya yi Odar gubar Bera tun daga kasar Sin domin Kashe Iyayen sa
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, bayan tsawon lokuta na laluben wannan mamaci sakamakon wuce ka'idar lokacin na komawar sa gida, an tsinci gawar sa ne rataye da igiya a saman itacen Kwakwa cikin dokar daji.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, an dakatar da wasu ma'aikatan lafiya hudu sakamakon bude kwakwalwar wani mutum bisa kuskure.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng