Nigerian news All categories All tags
Rashin imani: Yadda wata mata ta sace jaririn kurma a asibitin Dantsoho, Kaduna

Rashin imani: Yadda wata mata ta sace jaririn kurma a asibitin Dantsoho, Kaduna

Mun samu labarin cewa wata mata hatsabibiya maras imani ta sadada ta shiga asibitin gwamnati mallakin jihar Kaduna na Dantsoho ta kuma sace jariri, sabuwar haihuwa na wata mata kurma mai suna Salamatu Kabir.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily trust, an haifi jaririn ne a ranar 10 ga watan Janairun da ya gabata amma sai kuma ya bace sama-ko-kasa a ranar, kimanin awa daya kacal bayan haihuwar ta sa.

Rashin imani: Yadda wata mata ta sace jaririn kurma a asibitin Dantsoho, Kaduna

Rashin imani: Yadda wata mata ta sace jaririn kurma a asibitin Dantsoho, Kaduna

KU KARANTA: Yanzu ma muka fara neman mai a tafkin Chadi - Jami'ar Maiduguri

Sai dai mahaifyar jaririn da ta ga wadda ta sace shi amma ba bu halin magana ta siffanta ta da cewa doguwa ce, mai haske sannan kuma ta saje ne da sauran 'yan uwan ta inda ta yi awon gaba da shi kafin kowa ya farga.

Lamarin dai wanda ya ke cigaba da daure wa mutane kai, ya jawo suka da kuma Allaha-wadai daga bangarori na dai-daiku da kuma kungiyoyin mutane.

A hannu daya kuma, Kamar dai yadda muka samu, wani abun al'ajabi da ba kasafai ake samu ba ya auku a garin Kaduna dake a arewa maso yammacin kasar nan bayan da wata mata mai suna malama Hauwa'u Jamilu mai shekaru 24 a duniya ta haifi 'yan biyu duka mata amma daya na da hannaye 4 da kafa 3.

Malama Hauwa'u dake zaman matar malam Kabiru dake sana'ar Kafita, ta dai haihu gida ne kamar yadda muka samu a ranar Lahadin da ta gabata, ta watan jiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel