2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP

2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP

- Wata sabuwar rikici ta sake barkewa a jami'iyyar adawa ta PDP

- Dalilin haka tsohon ministan sadarwa, Jerry Ghana ya jagoranci wasu jiga-jigan jam'iyyar don sauya sheka zuwa SDP

- Suna zargin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da yin babakere cikin harkokin jam'iyyar ta PDP

Wasu tsaffin ministoci guda uku sun jagoranci wasu mambobin jam'iyyar PDP da dama yayin da sukayi hijira zuwa jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), wannan alama ce da ke nuna cewa sulhun da jam'iyyar ta PDP ta ke yi bai samu nasara kama yadda ya kamata ba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ministocin da suka fice daga jam'iyyar ta PDP sun hada da tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Jerry Gana, tsohon Ministan Ilimi, Tunde Adeniran da kuma tsohon Ministan Neja-Delta, Godsday Orubebe.

2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP
2019: Wasu tsaffin ministoci da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa SDP

Legit.ng ta gano cewa akwai wasu jiga-jigan na jam'iyyar PDP da za su bi sahun ministocin zuwa jam'iyyat ta SDP inda za su hada kai da jam'iyyar Peoples's Salvation Party (PSP) don hada karfi da karfe wajen kawar da jam'iyyar APC daga mulki a 2019.

KU KARANTA: Mutane 4 sun mutu a sabuwar rikicin da ta barke a Mambilla

Majiyar mu ta tattaro cewa tsaffin ministocin wanda suna cikin wandanda aka kafa jam'iyyar ta PDP da su ba su gamsu da yadda gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da ma wasu suke yin babakere cikin harkokin gudanar da jam'iyyar tun bayan taron jam'iyyar da aka gabatar a shekarar 2017 inda Uche Secondus ya zama sabon Ciyaman na jam'iyyar.

Adeniran yana daya daga cikin wanda sukayi takaran shiugabancin jam'iyyar amma ya sha wajen dan takarar gwamna Wike, wato Uche Secundus.

Tsaffin ministocin da sauran yan jam'iyyar PDP sun yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar ne bayan wani taro da suka fara a daren Alhamis 1 ga watan Maris kuma suka kamalla a ranar Juma'a 2 ga watan Maris a dakin taro na Ladi Kwali da ke Abuja.

Cikin wanda suka hallarci taron har da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki, tsohon ministan tsaro, Olu Agunloye, mataimakin kakakin majalisar jihar Ondo, Honarabul Dare Emiola, Tsohon hadimin shugaba Jonathan, Cif Mike Oghiadhome da dai sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164