Malamin Yahudun da yayi mafarki da Annabi ya musulunta
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani malamin Yahudu, da aka ambata da Michael Alexandre ya musulunta bayan mafarki da yayi da Annabin Allah.
Malamin wanda ya kasance daga tsatson Yahudawa mafiya kyamar Musulmai na Kiryat Arba, yayi shahada tare da alkawarin yiwa Musulunci hidima har iya rayuwarsa.
Da yake magana gaban manema labarai, ya yi kukan murna bayan ya ambaci kansa da suna Muhammad Mahdi.
Tuni dai Muhammadin Mahdi da ahlinsa baki daya suka zama musulunta.
KU KARANTA KUMA: Harin da yan Boko Haram suka kaiwa yan agaji a Rann, jihar Borno ya nuna cewa babu Allah a zukatansu
A wani lamari na daban Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace harin da aka kaiwa ma’aikatan dake bayar da agaji a Rann, jihar Borno, ya nuna karara cewa yan ta’addan Boko Haram basu da tsoron Allah, imani sannan sun cancanci a yi watsi dasu.
"Kamar yadda nake fadi a koda yaushe, babu addinin gaskiya da ya yarda da zaluntan bayin Allah. Kai hari da kahe wadanda ke bayar da agaji ga al’umma ya nuna tsangwaran rashin imani. Abun ki ne a wajen Allah da ma mutane.” Cewar shugaban kasar yayinda yake ta’aziyya ga majalisar dinkin duniya da sauran hukumomin bayar da agaji dake aiki a Rann, da kuma kasar baki daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng