Gwamnati ta fadada neman 'yan matan Dapchi zuwa kasashen Chadi, Nijar da Kamaru
- Gwamantin Tarayya ta fadada neman yan matan sakandire na Dapchi zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya
- Wannan ya bito bayan kwamitin tsaro da shugaban kasa ya kafa a ranar Alhamis ne wanda ta kunshi shugabanin hukumomin tsaro na kasar
- Shuwagabanin hukumomin tsaron na kasa duk sun tare a yankin na arewa maso gabas don hada karfi da karfe wajen ceto yan matan na Dapchi
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fadada neman daliban makarantar sakandiren kimiyya da fasaha na mata da ke Dapchi na Jihar Yobe zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, ne ya bayar da sanarwan a ranar Juma'a a Abuja.
Mohammed ya ce manyan shuwagabanin hukumomin tsaro su isa zuwa yankin na arewa maso gabas domin hada karfi da karfe wajen neman yan matan wanda a halin yanzu an fadada neman na nasu gaba da yankin na arewa maso gabas kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.
KU KARANTA: Dalilan da ya sa ban hallarci tarrukan APC ba - Saraki
Shugabanin da ya lissafo sun hada da Abayomi Olanisakin, shugaban tsaro na kasa, Ibok-Ete Ekwe Ibas; shugaban sojojin ruwa, Tukur Buratai; Shugaban sojojin kasa, da kuma Lawal Daura; Direktan Yan sandan farin kaya na DSS.
Shugabanin za su hadu ne da shugaban sojojin sama, Sadique Abubakar tare da mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Babagana Munguno (murabus) wanda tuni sun dade a garin na Yobe.
A farkon makon ne dai an samu rahotanni da ke nuna cewa an tafi da yan matan kasar Nijar ne.
A ranar Alhamis, Gwamnatin tarayyah ta kafa kwamiti tsaro don bincike kan yadda aka sace yan matan da kuma hanyoyin da za'a bi don ceto su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng