Buhari na aiki domin ganin an karyar da farashin shinkafa ga yan Najeriya - Bagudu

Buhari na aiki domin ganin an karyar da farashin shinkafa ga yan Najeriya - Bagudu

- Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce dukannin jihohin Najeriya 36 na iya noman shinkafa domin bayar da gudunmawa ga kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kawo chanji

- Bagudu ya bayyana cewa shugabancin shugaba Buhari don tabbatar da cewa kasar ta dogara da kanta wajen samar da isassun shinkafa da alkama

- Ya bayyana cewa idan samar da shinkafa a Najeriya zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga al’umman kasar

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar shugaban kasa kan samar da shinkafa da alkama ya ba yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen tabbatar da cewa akwai shinkafa sannan kuma kan farashi mai rahusa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Bagudu ya bayar da wannan tabbaci ne a lokacin da ya zanta da manema labarai bayan ganawa da kungiyar masu raba shinkafa na Najeriya (RIDAN) da kuma kungiyar Rice Millers Association of Nigeria (RIMAN) a Lagas a ranar Alhamis, 1 ga watan Maris.

A cewar Bagudu, da taimakon masu ruwa da tsaki, abun da yan Najeriya ke bukata ba wai talafin kudi wajen samar da shinkafa bane.

Buhari na aiki domin ganin an karyar da farashin shinkafa ga yan Najeriya - Bagudu

Buhari na aiki domin ganin an karyar da farashin shinkafa ga yan Najeriya - Bagudu

Ya ce samar da shinkafa kan farashi mai rahusa da kuma saukin samun shinkafar yar gida zai sa a samu ci gaba domin yan Najeriya sun fi neman yar waje.

KU KARANTA KUMA: Jami'ar ISM Adonai tace ba ta cikin sahun jami'o'i marasa inganci a Kasar Benin

Ya bayyana cewa idan ana samar da shinkafa a Najeriya zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga al’umman kasar.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na kokari don tabbatar da cewa kasar ta dogara da kanta wajen samar da isassun shinkafa da alkama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel