Buri na shine zuwa makarantar boko don in zama malami a garin mu, inji wani almajiri dan shekara 11
- Wani almajiri dan mai shekaru 11 a duniya ya bayyana burin sa na son zuwa makarantar boko
- Almajirin mai suna Usman Ya'u ya ce yana son ya zama malami ne idan har ya samu damar zuwa makarantar ta boko
- Ya'u ya yi kira da gwamnatoci su tabbatar da dokar kare hakkin yara wanda zai bawa kowa damar zuwa makaranta da samun kulawa mai kyau
Wani almajiri mai shekar 11 a duniya, Usman Ya'u. Ya fadi son zuciyarsa a rayuwa nasan zuwa makarantar boko kamar sauran yara don ya cin ma burin sa na zama malami.
Ya'u dan asalin jihar Katsina ya fada ne a Kamfanin dillanci labarai labarai ta kasa (NAN) a ranar Juma'a cewar iyayensa sun kawo shi Kaduna don koyan karatun Al'qurani a garin hayin dan mani dake Kaduna.
Yaron da yake magana cikin harshen hausa yace, yana son makarantarsa ta almajiranci amma bayasan bara yana kuma yana sha'awar makarantar boko harma wataran ace ya zama malami a kauyensu.
KU KARANTA: NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji
"Bana san bara amma ya zama dole saboda ta wannan hanyar kawai yake samun ci da sha"
"A duk sanda na fito bara, nakanga yara sa'annina sanye da kayan makarantar boko da jakar makaranta tare da kwandon daukar abincinsu wasunsu na turanci wanda ni bana fahimta.
"Nima inason zuwa makarantar boko dan na koyi turanci saboda inaso na zama malami a kauyenmu" a cewar yaron.
Lokacin da aka tambayeshi ko ya taba ko yasan dokar dake kare hakkin yara da walwalarsu a nan jihar Kaduna domin samarda kyakkyawan ilmin boko, lafiya tare da duk abinda zai gurbata yanayinsu, Ya'u yace bai san da zamarta ba.
Ni bansan da zaman wata doka dan karemu ba, kamar yadda kuke gani gamu nan da yawa muna bara a kan titi.
"Koda yake, ni ina rokon gwamnati ta tabbatar da wata doka ta yadda zata taimaka mani da duk wani mutumin da yakeso ya zama shugaban gobe."
NAN ta ruwaito cewa wannan dokar aita samu sahalewa tun a takwas ga watan Fabrairu daga majalisar dokoki ta jihar Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng