Kungiyar gwamnonin arewa sun goyi bayan kafa filayen kiwo
- Gwamnonin arewa sun jadada goyon bayan su ga shirin gwamnatin tarayya na kafa filayen kiwo don makiyaya a sassan kasar nan
- Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan sun kammala wata taro a gidan gwamnati na Kashim Ibrahim a Jihar Kaduna
- Gwamnonin sun lura cewa shanun da ake kiwon su a filayen kiwo a kasashen da suka cigaba sun fi samar da nama da madara fiye da namu da ake yawo da su
A ranar Alhamis ne kungiyar gwamnonin arewa suka bayyana cewa suna goyon bayan kirkirar gidajen kiwo don magance rikice-rikicen da ke faruwar tsakanin manoma da makiyaya a sassan kasar nan.
Baya ga kawo karshen rikicin, gwamnonin sun kuma ce gidajen kiwon za su za'a samu karuwar adadin madara da nama da dabobin za rika samar wa ga arewa da ma sauran sassan kasar baki daya.
KU KARANTA: NAHCON ta gargadi maniyyata su kasance masu biyaya ga doka yayin aikin hajji
Gwamnonin sun bayar da wannan sanarwan ne a garin Kaduna a inda suka gudanar da wani taro a gidan gwamnati na Kashim Ibrahim. Shugaban kungiyar Gwamna Kashim Ibrahim ya lissafo alkhairan da ke tattare da kafa gidajen kiwon.
Ya ce, "A kasashen da suka cigaba, sa guda na samar da madara lita 40 a rana amma namu nagida Najeriya bata samar da madarar da ta dara lita daya."
A sakon da suka bayar a karshen taron gwamnonin sun suna goyon bayan gwamnaytin Muhamammadu Buhari dari bisa dari a kokarinda takeyi wajen kawo karshenrikcin makiyaya da manoman.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng