Jami'ar ISM Adonai tace ba ta cikin sahun jami'o'i marasa inganci a Kasar Benin

Jami'ar ISM Adonai tace ba ta cikin sahun jami'o'i marasa inganci a Kasar Benin

- An yi wa Jami’o’in Kasar Benin da dama shaidar banza yanzu a Duniya

- Wata Jami’a mai suna ISM Adonai ta fitar da kan ta daga wannan sahu

- Jami’ar ta ISM Adonai tace manyan Hukumonin Duniya sun yarda da ita

Mun samu wani rahoto na musamman cewa wasu Makarantu a Garin Kotono cikin Jamhuriyyar Benin sun tsame kan su daga cikin sahun bara-gurmin Jami’o’in da ke kasar. A baya an yi wa Jami’o’in kasar kudin goro saboda rashin ingancin wasun su.

Jami'ar ISM Adonai tace ba ta cikin sahun jami'o'i marasa inganci a Kasar Benin
Jami'ar ISM tace ban da ita a cikin yin Digirin bogi

A kwanakin baya wasu Jaridu a Najeriya sun sa Jami'ar ISM Adonai cikin jerin jami'o'in da basu da inganci a kasar Benin. Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar ta barranta kan ta daga wannan zargi inda tace ba ta cikin ruba-ruban Jami’o’in da ke Benin.

KU KARANTA: Jerin manyan masu kudin Nahiyar Afrika a shekarar 2018

Jami’ar ta ISM Adonai tana da shaidar cancanta daga Hukumomin Duniya. Har irin su hukumar tantance makarantun kasuwanci ta Amurka tayi na’am da ingancin wannan Makaranta inda aka ba ta lamba a 2015 saboda darajar kwas kwasan ta da tsare-tsare.

Jami’ar ta wanke kan-ta lokacin da ta aika takarda ga Hukumar NUC mai kula da Jami’oin Najeriya da ma Ma’aikatar ilmi domin tona asirin Mutanen Najeriya da ke karatu ba bisa ka’ida ba. Wasu Makarantun kasar dai kafin kace cas sai ka ji an kammala Digiir.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel