Jerin manyan masu kudin Nahiyar Afrika a shekarar 2018
- A kaf afrika Aliko Dangote na Najeriya bai da sa’a har yanzu
- Dangote dai ya ba sama da Dala Biliyan 10 baya tun ba yau ba
- Akwai wasu ‘Yan Najeriya 3 cikin manyan Attajiran Nahiyar
Mujallar Forbes ta fitar da rahoto inda aka ‘Dan kasuwar Najeriya Aliko Dangote ne sahun gaba a cikin jerin Attajiran da ke Nahiyar Afrika. Shekaru 7 kenan a jere an rasa wanda zai iya shan gaban Hamshakin ‘Dan kasuwar a kaf Nahiyar.
Dama can kun ji cewa Aliko Dangote ne gaba inda ya ba Dala Biliyan 12 baya. Akwai wasu ‘Yan Najeriya a jerin irin Mike Adenuga da Folorunsho Alakija. Ga dai cikakken jerin nan na masu kudi da dukiyar da su ka taka kamar haka:
KU KARANTA: An tura mutane horo a kasar waje domin shiryawa Kamfanin Dangote
1. Aliko Dangote – $12.2
2. Nicky Oppenheimer – $7.7
3. Johann Rupert – $7.2
4. Nassef Sawiris – $6.8
5. Mike Adenuga – $5.3
6. Issad Rebrab – $4
7. Naguib Sawiris – $4
8. Koos Bekker – $2.8
9. Isabel dos Santos – $2.7
10. Mohamed Mansour – $2.7
11. Patrice Motsepe – $2.4
12. Aziz Akhannouch – $2.2
13. Yasseen Mansour – $1.9
14. Strive Masiyiwa – $1.7
15. Folorunsho Alakija – $1.6
16. Othman Benjelloun – $1.6
17. Mohammed Dewji – $1.5
18. Youssef Mansour – $1.4
19. Michiel Le Roux – $1.2
20. Stephen Saad – $1.2
21. Desmond Sacco – $1.1
22. Onsi Sawiris – $1.1
23. Christoffel Wiese – $1.1
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng