An sayi zanen wani dan Najeriya akan kudi Naira Miliyan 508
- An sayi zanen wani dan Najeriya akan kudi sama da N508m
- Zanen na wata Gimbiya an yi shi tun a shekarar 1974
- Zanen ya bata tun bayan mutuwar wanda yayi zanen Mista Ben Enwonwu
An sayi zanen wani dan Najeriya akan kudi sama da dala miliyan daya da rabi, wanda wani kwararren mai zane yayi.
Ben Enwonwu shine yayi zanen na wata gimbiya, da ake kira Tutu a kudancin Najeriya a shekarar 1974.
DUBA WANNAN: Majalisar Dattawa ta dora laifin jinkirin kasafin kudi akan ministocin kasar nan
Masana sun ce rabon da a ga zanen tun a shekarar 1974 din a lokacin da aka yi tallar shi a Legas, sai kwanan nan da aka ganshi a wani gidan ajiye kayan tarihi a birnin Landan.
A kwanan nan dai, manyan kasashen duniya na nuna sha'awar zanen da ake yi a Najeriya sannan kuma darajarsu ta karu.
Wani shahararren marubucin littafi Ben Okri, wanda ya taba cinye gasar rubuta littafi na booker ya bayyana zanen a matsayin wani abu mai muhimmanci da aka samo a fasahar zane a nahiyar Afrika a cikin shekaru 50 da suka wuce.
Mista Enwonwu ya yi zanen gimbiya Tutu har guda uku, sai dai kuma duka sun bata bayan mutuwarsa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng