Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke masu garkuwa da mutane a Imo

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke masu garkuwa da mutane a Imo

- Rundunar ‘Yan Sanda ta damke masu addabar Jama’a a Jihar Imo

- An kama masu laifi sama da 50 dauke da manyan makamai a Jihar

- Wadannan mutane sun kware wajen satar jama’a d fashi da makami

Mun samu labari daga Information Nigeria cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke masu garkuwa da mutane sama da 50 da ake zargi da laifin fashi da makami da ‘yan sace-sace da sauran su.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya sun damke masu garkuwa da mutane a Imo
Manyan masu laifi sun shiga hannun Jami'an tsaro

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo sun kama wadanda su ka fitini Jama’a da satar dukiya da kananan yara har ma da bada shaidar zir da kuma aikin shan jini. Yanzu haka dai an damke wannan mutane da manyan makamai.

KU KARANTA: An kashe wani jagoran Sojojin Najeriya a filin daga

Jami’an ‘Yan Sandan kasar sun bayyanawa Duniya irin manyan makaman da aka damke wadannan mutane da su da kuma motocin sata da dama. Manema labarai sun dauki hotunan wadannan kaya da aka samu a wajen su.

Dama can irin wadannan hatsabiban mutane sun fitini Jama’a a Jihar Imo da kananan sata har ma da fashi da makami da kuma tsare mutane su na garkuwa da su har da kananan yara har sai an biya makudan miliyoyin kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel