Jami'an tsaro sun hallaka wani gagararren barawon shanu a Zamfara mai suna 'janar Buhari'

Jami'an tsaro sun hallaka wani gagararren barawon shanu a Zamfara mai suna 'janar Buhari'

- Jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula a hannun 'yan bindiga da 'yan fashi da kuma barayin shanu

- A cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a jihar, jami'an tsaron farin kaya (DSS) sun hallaka wani gagararren barawon shanu da ake kira 'janar' Buhari

- Haka a kudancin Najeriya, jami'an tsaron sun yi nasarar kama wani gagararren mai garkuwa da mutane, Anthony Kio Elegwe

Kamar yadda ku ka sha karantawa a labaran Legit.ng, jihar Zamfara ta dade tana fama da tashe-tashen hankula a hannun 'yan bindiga da 'yan fashi da ma barayin shanu.

A cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a jihar, jami'an tsaro sun yi nasarar kashe wani gagararren barawon shanu da ake kira 'janar Buhari' wanda hukumar DSS ta ce sunan sa na gaskiya Umar Abubakar. An kashe shi tare da wani da su ke aikata laifi tare a karamar hukumar Adavi dake jihar Kogi.

Jami'an tsaro sun hallaka wani gagararren barawon shanu a Zamfara mai suna 'janar Buhari'
Jami'an tsaro

A wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar bakin Tony Opuiyo, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin hukumar, ya ce sun yi nasarar damke wani Isiah Suwe, abokin gagararren mai garkuwa da mutanen, Terwase Awkaza, a jihar Binuwai.

KARANTA WANNAN: Allah ya kubutar da wata dalibar sakandiren Dapchi, ta ci wani al-washi

Kazalika hukumar ta ce ta yi nasarar damke wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a kudancin Najeriya da ake kira Anthony Kio Elegwe, mai shekaru 37, dan asalin Oyigba dake karamar hukumar Ahoada ta yamma a jihar Ribas. An kama shi ne a jihar Bayelsa ranar 22 ga watan Fabrairu.

Kazalika hukumar ta a ce ta kama masu aikata laifuka daban-daban tare da kama makamai masu tarin yawa daga hannun 'yan ta'addar a sassan kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng