Shugaba Buhari ya karbi sabbin Jakadun kasashen ketare 3 a fadar sa
A yau 1 Maris, 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi sabbin jakadun kasashen ketare uku zuwa Najeriya a fadar sa ta Villa dake babban birni na tarayya.
Fadar ta shugaban kasa ta bayyana wannan rahoto da sanadin shafin ta na dandalin sada zumuntar Facebook mai sunan Aso Rock Villa.
KARANTA KUMA: Kwamishinan Kwankwaso zai gurfana gaban Alkali da laifin Zambar N47.8 a ranar 8 ga watan Maris
Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya karbi jakadun uku a fadar sa da suka hadar da; na kasar Singapore; Mista Lim Sim Seng, na kasar Uganda; Mista Nelson Ocheger da kuma jakadiyar kasar Philippines; Mis Shirley Ho Vicario.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng