Nigerian news All categories All tags
Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

- Masana binciken tarihi sun gano wasu wasu kabarburan manyan sarakunan zamanin baya na kasar Masar

- Masanan sun gano cewa wasu daga cikin mutanen an birne su ne tun zaman Firauna na farko a wani birni da ke kudancin Al-Kahira

- Masu binciken sunyi karo da wani abin mamaki ranar jajibirin sabuwar shekara yayin da suka tono wata kabari mai dauke da rubutu da ke bushara da shiga sabuwar shekara

Masu binciken tarihi sun gano wasu manyan kabarburan sarakunan zamanin baya a kasar Masar masu dauke da akwatunan gawawaki har ma daya daga cikin akwatunan na dauke da sako daga barzahu.

Makabartar wadda ta fi shekaru 2,000 tana kusa da birnin Minya ne a kudancin birnin Alkahira. Masannan suna sa ran za'a shafe wasu shekaru biyar nan gaba kafin a gama tone makabartar.

Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Kamar yadda Ministan adana kayayakin tarihi Khaled al-Enany ya ce an sami akwatunan gawawaki wanda adadin su ya kai 40 wanda aka gina da duwatsu da kuma tukwane da sauran kayan alatu.

KU KARANTA: Za'a hukunta masu yadda kalaman kiyaya ta hanyar rataye - Majalisar Dattawa

Al-Enany ya ce wasu daga cikin kaburburan an binne mutanen cikin ne tun zamanin Fira'auna na farko zuwa sauaran firaunonin da suka biyo kusan shekaru 300 gabanin zuwan Annabi Isa.

Shugaban masu binciken kayayakin tarihi Mostafa Waziri ya ce mafi yawancin kaburburan da aka gano na masu bautan wani tsohon abun bauta na mutanen Masar ne mai suna Thot.

Ya kuma ce an samu wasu bangarorin jikin mamatan a tuluna ne da akayi wa ado da rubutu mai dauke da sunayen mammatan.

Ya kuma bayyana yadda masu binciken sukayi karo da wani abin mamaki na samun wata laya a ranar jajibiren sabuwar shekara wadda aka rubuta "barka da sabuwar shekara" a jikinta da harshen mutanen Masar na da.

Hakan yasa ya furta cewa: "Wannan sako ne aka aiko wa al'ummar duniya daga barzahu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel