EFCC ta nemi Kotu ta daure tsohon Gwamnan Jihar Taraba a kurkuku
- Tsohon Gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame zai san matsayin sa a Ranar 30 ga Watan Mayu
- Hukumar EFCC ta maka shi Kotu da zargin satar dukiyar al’umma a lokacin yana Gwamna
- Yanzu dai EFCC ta bankado duk shaidun ta sai dai Alkali Adebukola Banjoko ya dage shari’a.
Ana cigaba da shari’a da Tsohon Gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame wanda ake zargi da tafka muguwar satar da ta haura Naira Biliyan 1 a lokacin yana kan kujera.
Hukumar EFCC tana karar Jolly Nyame bisa zargin cin amana da karkatar da kudin Gwamnati tun 2010. Lauyan da ya shigar da karar Rotimi Jacobs ya kawowa Kotu shaidu akalla 14 da su ka tabbatar da zargin da ke kan wuyan tsohon Gwamnan.
KU KARANTA: Ma'aikatan shari'a sun rufe ofishin Alkalan Alkalai
Lauyan da ke kare tsohon Gwamnan watau Olalekan Ojo ya bayyanawa Kotu cewa ayi watsi da shaidar da EFCC ta kawo domin akwai tafka-da-warwara a bayanan. Lauyan yace babu wata hujjar gaske da ke nuna cewa Nyame ya saci kudin Jihar Taraba.
EFCC na zargin Nyame da sace Naira Biliyan 1.641 a lokacin yana Gwamna don haka aka nemi Alkali mai shari’a ya garkame shi cikin gidan yari ba tare da bata lokaci ba. Yanzu dai an dage shari’ar har sai nan da wata uku sannan za a kuma zama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng