Gwamnatin Buhari za ta koma neman danyan mai a Tafkin Chadi
- Gwamnatin Buhari na kokarin gano danyan mai a Yankin Arewa
- A baya an dakatar da wannan aiki saboda sha’anin rashin tsaro
- Yanzu za a koma bakin aiki a Yankin gadan-gadan inji Dr. Baru
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jim kadan da ceto Ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da ‘Yan Boko Haram su ka tsare kwanakin baya, NNPC za ta cigaba da kokarin hako danyan man fetur a Yankin Chadi bayan tsaro ya dan yi sauki.
Shugaban Kamfanin NNPC na Najeriya Dr. Maikanti Kacalla Baru ya bayyana cewa sun kammala shirin da su ke yi na komawa Yankin Chadi domin cigaba da kokarin gano danyan man fetur wanda a da an tsaida wannan aiki.
KU KARANTA: Boko Haram sun saki bidiyon Ma’aikatan da su ka sace a Maiduguri
Baru ya jagoranci Ma’aikatan NNPC na kasar zuwa kasuwar baja-koli ta Duniya a Garin Kaduna a makon nan inda ya bayyana cewa sun gano inda za a iya dacewa da arzikin fetur a Yankin Benuwe da ke tsakiyar kasar nan.
Yanzu dai dar-dar din da ake ciki na tsaro ya lafa don haka za a koma aiki. Baru yace za a koma bakin aiki, kuma za ayi kokarin gano man da ke Yankin Yankari da kuma Jihar Kogi da Nasarawa da kuma irin su bangaren Jihar Neja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng