Majalisar Dattawa ta dora laifin jinkirin kasafin kudi akan ministocin kasar nan

Majalisar Dattawa ta dora laifin jinkirin kasafin kudi akan ministocin kasar nan

- A jiya ne Majalissar Dattijai ta kasa ta dora laifin jinkirin kaddamar da kassafin kudi na shekarar 2018 akan ministocin kasar nan

-Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bada daga nan zuwa juma'ar mako mai zuwa akan a gabatar da kasafin kudin

Sanatoci sun dora laifin jinkirin kasafin kudi akan ministoci
Sanatoci sun dora laifin jinkirin kasafin kudi akan ministoci

A jiya ne Majalissar Dattijai ta kasa ta dora laifin jinkirin kaddamar da kassafin kudi na shekarar 2018 akan ministocin kasar nan.

Shugaba Muhammamdu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin N8.6tr a taron majalissar tarayya a ranar 7 ga watan Nuwamban bara. Ma’aikatar tayi niyyar dawo da kasafin kudin zuwa watan Janairu ko watan Disamba.

DUBA WANNAN: Wata ta hannun daman shugaba Donald Trump ta ajiye aikin ta

An baiwa Ministoci da Shugabannin Hukumomi mako daya domin su gabatar da kasafin kudin. Wa’adin zai kare juma’a ta gaba.

A lokacin taron, Shugaban Majalissar Dattijai, Bukola Saraki, ya nemi Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai , Sunny Ogbuoji (PDP, Jihar Ebonyi) don yayi bayanin yadda kwamitin ta tsara kasafin kudin.

Ogbuoji ya ce an samu jinkirin gabatar da kasafin kudin daga wurin ministoci da shugabannin hukumomi.

"Mafi yawan cin kwamitocin suna da babban kalubale da hukumomin MDAs saboda yawancin su basu zuwa domin su tattauna da su. Wasu ministocin sai su ce muku sun bar kasar, dalilin hakan sai abin ya zama duka ba wani tsari.

"Har ila yau, wasu daga cikin MDAs, idan aka nemi suje suyi aiki akan abin da suka kawo, da yawa daga cikin su basa dawowa. Abinda yake kawo jinkiri kenan a wurin aikin. Kuma shine dalilin da ya saka bamu da cikakken rahoto har zuwa yau," in ji shi.

Saraki ya bawa MDAs zuwa ranar juma'ar mako mai zuwa akan su gama tattaunawa da kwamitin majalisar dattijai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng