Wata ta hannun daman shugaba Donald Trump ta ajiye aikin ta

Wata ta hannun daman shugaba Donald Trump ta ajiye aikin ta

- Daraktar harkokin sadarwa ta fadar White House ta yi murabus

- Shugaba Donald Trump ya fadi hakan jiya a wani jawabi da yayi

- Hope Hicks mai shekaru 29, ta kasance daraktar hukumar sadarkar a fadar White House, sannan ta kasance mafi kuruciya a tarihin fadar shugaban kasar

Wata ta hannun daman shugaba Donald Trump ta ajiye aikin ta

Wata ta hannun daman shugaba Donald Trump ta ajiye aikin ta

Daraktar hukumar sadarwa ta fadar shugaban kasar Amurka wato White House, sannan kuma daya daga cikin na hannun daman shugaba Donald Trump, Hope Hicks, ta ajiye aikin ta.

DUBA WANNAN: An kafa kwamitin binciken 'Yan matan Dapchi a jiya

Shugaba Donald Trump ya fadi hakan jiya a wani jawabi da yayi, "Hope tayi fice, ta yi ayyukanta cikin tsari da amana a shekaru ukun da suka gabata. Tana da hangen nesa ga basira, zanyi jimamin ajiye aikin ta matuka. Ta same ni da kudurin cewa tana so ta maida hankalinta akan wasu ayyuka, tayi min bayani kuma na fahimta. Na saka a raina cewa zan sake aiki tare da ita a nan gaba".

Hope Hicks mai shekaru 29, ta kasance daraktar hukumar sadarkar a fadar White House, sannan ta kasance mafi kuruciya a tarihin fadar shugaban kasar, akwai tambayoyin da kwamitin tattara bayanan sirri ta yi mata a ranar Talata, wanda taki amsa su.

Hicks ta bayyana wa kwamitin cewa, a wasu lokutan akan bukaceta data danne gaskiyar abinda ke faruwa, sai dai tace bata taba yin karya akan abinda ya shafi binciken da ake zargin kasar Rasha da aikatawa a zaben shugaban kasar na shekarar 2016, wanda shugaba Donald Trump ya lashe a karkashin jam''iyyar Republican.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel