Yusuf Buhari ya sadu da mahaifinsa bayan dawowa daga hutun jinya (hotuna)
- Dan shugaban kasa Yusuf Buhari ya dawo daga hutun jinya
- Ya hadu da mahaifinsa shugaban kasa Muhammadu Buhari
Rahotanni dake zuwa mana ya nuna cewa dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf ya dawo daga hutun jinya da ya tafi.
Bayan dawowar nasa ya sadu da mahaifin nasa domin yi masa gaisuwa na musamman.
Buhari Sallau ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na Facebook inda yake cewa: “Yusuf Muhammadu Buhari Yana Gaisheda Babanshi Shugaba Buhari Bayan Dawowanshi Daga Hutun Jinya, Alhamdulillah”.
A cikin watan Janairu ne, Yusuf Buhari, yayi hatsari akan babur inda ya samu mumunar rauni. Da farko an fara jiyar sa a asibitin Cedacrest dake Abuja kafin aka garzaya da shi kasar Jamus.
Karin hotuna daga dawowarsa:
KU KARANTA KUMA: Jerin sababbin fim din Hausa a 2017-2018
A baya Legit.ng ta kawo cewa Dan shugaban kasa, Muhamadu Buhari, Yusuf, ya dawo Najeriya a ranar Litinin bayan ya jinya a kasar waje.
Yusuf Buhari, ya samu lafiya sosai, kuma zai cigaba da rayuwar sa kamar yadda ya saba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng