An yaye tubabbun 'yan Boko Haram 95 a jihar Gombe
- 95 cikin 254 na tubabbun 'yan Boko Haram sun samu horaswa a sana'o'in dogaro da kai daban-daban
- Sun dauki tsawon watanni 4 su na koyon sana'o'in wanda daga karshe za a ba su kayan aiki da jari don su kafa kan su
- Birgediya-Janar Bamidele Shafa, jami'in gudanar da shirin koyar da sana'o'in, shi ne ya bayyana hakan
Rundunar Soja ta 'Operation Safe Corridor' mai kula da tubabbun 'yan Kungiyar Boko Haram, ta samu nasarar yaye 95 cikin 254 na tubabbun wadanda a ka horas da sana'o'in dogaro da kai daban-daban na tsawon watanni hudu a Jihar Gombe.
Birgediya-Janar Bamidele Shafa, jami'i mai gudanar da shirin koyar da sana'o'in, ya ce an horas da su ne a fannonin sana'anta kayan shafe-shafe da wanzanci (aski) da kuma hada takalma.
KU KARANTA: Hukumar Soji ta hada gwiwa da manoma da masunta wurin neman 'yan matan Dapchi
Shafa ya ce da sannu za a fara koyar da dinki da kafintanci da walda da kiwon kifi da kaji. Ya kuma ce za a gabatar da wadanda a ka yaye zuwa ga Hukumar Ayyukan yi na kasa (NDE), reshen Jihohin su don su cigaba da samun horo.
Kwamandan Sansanin Horaswan, Kwanel Adetuyi Moses, ya ce 20 daga cikin 95 din kananan yara ne. Ya kuma ce an horas da su ne cikin sakewa da nishadi. Ya kuma bayyan cewar sun nuna hali mai kyau da natsuwa yayin zaman su sansanin.
Ita kuma Hukumar Tsaro ta Kasa ta ce za a ba wa kowannen su kayan aiki da kudin yin jari don ya kafa kan sa a sana'ar da ya koya domin dogaro da kai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng