INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zabe na shekaru 36 masu gabatowa

INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zabe na shekaru 36 masu gabatowa

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar Zabe ta kasa wato INEC, ta fitar da taswiri tare da jadawalin gudanar da zaben kasa na Najeriya na tsawon shekaru 36 masu gabatowa daga shekarar 2019 zuwa 2055.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shine ya bayyana hakan a wata ganawa da shugabannin jam'iyyu na kasa a babban birni na tarayya.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu

Da sanadin jaridar The Punch, Legit.ng ta kawo muku ranakun gudanar da zabe kasa na shekaru 36 da hukumar ta fitar:

A shekarar 2019; za a gudanar da zaben a ranar 16 ga watan Fabrairu da kuma 2 ga watan Maris.

A Shekarar 2023; za a gudanar da zaben a ranar 18 ga watan Fabrairu da kuma 4 ga watan Maris.

A Shekarar 2027; za a gudanar da zaben a ranar 20 ga watan Fabrairu da kuma 6 ga watan Maris.

A Shekarar 2031; za a gudanar da zaben a ranar 15 ga watan Fabrairu da kuma 1 ga watan Maris.

A Shekarar 2035; za a gudanar da zaben a ranar 17 ga watan Fabrairu da kuma 3 ga watan Maris.

A Shekarar 2039; za a gudanar da zaben a ranar 19 ga watan Fabrairu da kuma 5 ga watan Maris.

A Shekarar 2043; za a gudanar da zaben a ranar 21 ga watan Fabrairu da kuma 7 ga watan Maris.

A Shekarar 2047; za a gudanar da zaben a ranar 15 ga watan Fabrairu da kuma 2 ga watan Maris.

A Shekarar 2051; za a gudanar da zaben a ranar 18 ga watan Fabrairu da kuma 1 ga watan Maris.

A Shekarar 2055; za a gudanar da zaben a ranar 20 ga watan Fabrairu da kuma 6 ga watan Maris.

Farfesa Mahmood ya ci gaba da cewa, wannan tsari na fitar da jadawalin gudanar da zabe ya samo tushe ne daga kasashen da suka ci gaba ta fuskar Dimokuradiyya.

KARANTA KUMA: Majalisar dinkin Duniya ta fusata akan 'Yan Matan Dapchi, za ta tallafawa Najeriya

Ya kara da cewa, cikin mako guda da ya gabata, hukumar ta karbi takardu na neman izinin kafa sabbin jam'iyyu 108 a fadin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani kwamishinan tsohuwar gwamnati zai gurfana gaban babbar kotun jihar Kano a ranar 8 ga watan Maris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng