Hukumar Soji ta hada gwiwa da manoma da masunta wurin neman 'yan matan Dapchi

Hukumar Soji ta hada gwiwa da manoma da masunta wurin neman 'yan matan Dapchi

- Hukumar Soji ta nemi taimakon manona da masunta masana yankin Dapchi don neman 'yan matan da a ka sace

- Shugaban aikin soji na Lafiya Dole, Manjo-Janar Nicholas Rogers, shi ne ya bayyana hakan

- Rogers ya ce Gwamnati ta himmatu wurin kubutar da 'yan matan don kuwa babu dare babu rana neman su a ke yi

Manjo Janar Nicholas Rogers, Shugaban Kwantar da Tarzoma na Lafiya Dole, ya ce Hukumar Soji ta hada karfi da karfe da manoma da masunta don neman 'yan matan Dapchi da a ka sace.

Ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Talata yayin kaddamar da sabbin gine-gine a Barikin Sojin Sama na garin Monguno, wanda Mai Bayar da Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno ya kaddamar.

Hukumar Soji ta hada gwiwa da manoma da masunta wurin neman 'yan matan Dapchi
Hukumar Soji ta hada gwiwa da manoma da masunta wurin neman 'yan matan Dapchi

KU KARANTA: Kudurin kirkirar Peace Corps: Majalisar wakilai ta yi alla-wadai da kin amincewar Buhari

Rogers ya ce babu dare babu rana, neman 'yammatan a ke yi. Ya jaddada cewar Gwamnati ta ba neman 'yan matan matukar muhimmanci. Ya kuma ce a halin yanzun an bata awanni 200 don neman su ta kasa da ta sama.

Ya ce NSA da Babban Hafsan Sojin Sama ba su yi kasa a gwiwa ba don har da su a ka fita shawagin neman 'yan matan ta jirgin sama. Zuwan na su kuma zaburarwa ne don himmatuwa wurin neman 'yan matan.

Ya kuma ce NSA ya gabatar ma su da manoma da masunta wadanda su ka san yankin da kyau don su taimaka wurin neman 'yan matan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164