Harin Adamawa: Sojoji sunyi arangama da makiyaya, mutane 10 sun mutu

Harin Adamawa: Sojoji sunyi arangama da makiyaya, mutane 10 sun mutu

Dakarun sojoji sun arangama tare da kashe wasu mutane 10 da ake zargin makiyaya ne bayan sun kai hari kauyen Gwamba dake karamar hukumar Demsa na jihar Adamawa.

Kakakin rundunar soji Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.

Ya ce dakarun bataliya na musamman dake gudanar da aikin Ayem Akpatuma (Cat Race) da aka tura karamar hukumar Numan sun amsa wani kiran gaggawa a ranar Talaata sannan sun taimakawa abokan aikinsu a kauyen Gwamba da mahara suka kai hari.

Duk da kokari da akayi na ceto kauyen daga halaka, Birgediya Janar Chukwu ya bayyana cewa mayakan sun sanya ma kauyen wuta kafin sojoji sui so.

Harin Adamawa: Sojoji sunyi arangama da makiyaya, mutane 10 sun mutu
Harin Adamawa: Sojoji sunyi arangama da makiyaya, mutane 10 sun mutu

A halin yanzu dakarun sojin sun dakile maharan sannan sun kama shida daga cikinsu a kauyen Garigiji yayinda suke kokarin tserewa.

KU KARANTA KUMA: Yan fashi sun kai harin bazata ga yan kasuwa a Zamfara, 3 sun bata

Abubuwan da aka samo sun hada da bindigar AK 47 guda daya, harsasai, babur daya da sauran su.

A wani lamari na daban, wasu da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai harin bazata ga motocin yan kasuwa dake hanyar zuwa garin Dansadau a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng