Gangar danyen man fetur ya kara kudi zuwa Dala $63.91
- Farashin gangar danyan mai ya tashi a kasuwar Duniya
- Danyan man Najeriya ya kusa kai Dala $64 a makon nan
- Kasar Saudi ta rage hago danyan man fetur a watan nan
A farkon makon nan ne mu ka ji cewa Danyen mai yayi wani ‘dan-karen tashi a karshen wannan watan na Fubrairu. An dai yi kusan wata guda kenan ba a ga mai yayi irin wannan tsada ba.
Gangar danyen man fetur ya kara kudi Ranar Litimin a kasuwar Duniya. A yanzu haka abin da mu ke ji shi ne ya haura Dala $63.91 kan kowane ganga. Dalilin hakan kuwa shi ne yanzu ana neman man matuka a Duniya musamman a Kasar Amurka.
KU KARANTA: 'Yan kasuwar canji na saida Dalar Amurka a kan N362
Man Najeriya dai ya kai kusan Dala $67.50 a kasuwannin Duniya a makon nan. An dauki fiye da makonni uku, man na Najeriya bai yi kudi haka ba. Kasar Saudi dai ta bayyana cewa za ta rage yawan abin da ta take hakowa a kowace rana yanzu.
Dama masu harsashe sun ce a bana za a saida man ne a kan Dala $60 zuwa $70. A Kasar Turai ma dai ana bukatar man fetur yayin da kasashen OPEC masu arzikin na mai ke kokarin rage hannu domin farashin man ya dan karu a kasuwar Duniya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng