Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da iyalan wani dan jarida, sun kashe makwabcin sa a jihar Kaduna
Rahotanni da sanadin jaridar Vanguard sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da iyalan wani dan jarida na VOA (Voice of America) da suka hadar da matar sa da kuma dan sa guda a garin Kaduna a ranar Larabar da ta gabata.
Wannan 'yan ta'adda sun kuma salwantar da rayuwar wani ma'aikacin hukumar kula da manyan hanyoyi ta FRSC da ya kasance makwabcin wannan dan jarida a yayin da yayi yunkurin sauke nauyin hakkin makwabtaka na kawo dauki.
Dan jaridar, Mallam Nasir Birnin-Yero, ya shaidawa manema labarai cewa, wannan 'yan ta'adda kimanin su 30 sun kai hari gidan sa dake Birnin-Yero da misalin karfe 1.30 na dare.
KARANTA KUMA: 'Matsin tattalin arziki ya sanya nake fashi da makami'
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan dai sun je neman wannan dan jarida ne, inda basu tarar da shi ba sai mai dakin sa da kuma dan sa guda da suka yi awon gaba da su.
A yayin haka ne makwabcin sa da ya kasance ma'aikacin hukumar FRSC, Sabitu Abdulhamid, ya yi yunkurin sauke nauyin makwabtaka da ya rataya a wuyansa, sai dai 'yan ta'addan sun ci karfin sa da har suka sheka shi barzahu.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, matsain tattalin arziki ya jefa wasu matasa afkawa fashi da makami a jihar Neja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng